(ABNA24.com) Kungiyar Tarayyar Afrika AU, za ta kira taron samar da kudi, na bangarori masu zaman kansu na nahiyar da masu bada gudunmuwa, domin taimakawa aikin tunkarar cutar Ebola dake gudana a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
AU wadda ta jadadda matukar damuwarta kan batun yaduwar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ta bayyana cewa, za ta kira taron manyan jami'ai mai taken : "asusun hadin kai na Afrika, domin yaki da Ebola" a farkon makon watan Satumban bana, da nufin samar da abubuwan da ake bukata na tunkarar Ebola a nahiyar.
Sanarwar da AU ta fitar, ta ce ana sa ran taron wanda zai gudana karkashin shugaban hukumar kula da ayyukan tarayyar, Moussa Faki Mahamat, zai hada wakilan bangarori masu zaman kansu na fadin nahiyar da kuma abokan hulda da masu bada gudunmuwa na kasa da kasa.
Ko a baya ma, AU ta shirya taron samar da kudi na nahiyar a shekarar 2014 kan batun, a lokacin da Ebola ta barke a kasashen yammacin nahiyar.
/129
29 Yuli 2019 - 03:59
Lambar labari: 965487
Kungiyar Tarayyar Afrika AU, za ta kira taron samar da kudi, na bangarori masu zaman kansu na nahiyar da masu bada gudunmuwa, domin taimakawa aikin tunkarar cutar Ebola dake gudana a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.